Shugaba Buhari ya Taya IBB Murnar Kara Shekara a Duniya

 

Shugaban Kasa,Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban Najeriya, Ibrahim Babangida murnar kara shekara a Duniya.

Tsohon Shugaban na mulkin soja ya na bikin murnar isa shekara 80 da haihuwa.

Shugaban Najeriya ya yi jawabi, ya yabi IBB, ya yi masa fata ya kara tsawon rai.

Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Me Garba Shehu ya fada a jawabinsa?

Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin babban mai ba shi shawara wajen yada labarai da hulda da jama’a, Malam Garba Shehu.

The Nation ta rahoto Garba Shehu yana cewa shugaba Muhammadu Buhari sun yi tarayya da Ibrahim Babangida wajen ganin kasa ta gyaru. Buhari ya yi kira ga Babangida da ire-irensa, su dage wajen ganin Najeriya ta yi nasarar kai ga ci.

“Muhammadu Buhari ya aika sakon taya murnarsa ga tsohon shugaba Ibrahim Babangida, ya na masa afatan tsawon rai yayin da ya ke cika shekara 80.”

“Shugaban kasa Buhari ya ce a matsayinsu na tsofaffin sojojin yaki da suka yi ritaya, duk sun hadu a wajen fatan alheri da sha’awar ganin an samu hadin-kai a Najeriya.”

“Shugaban kasa Buhari ya na sa ran cewa manyan mutane irinsu tsohon shugaba Babangida da ire-irensa za su taimaka wajen taimakon kasar ga nasara, da cigaba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here