Shugaba Buhari ya Tsawaita Wa’adin Babban Kwanturolan Hukumar Kula da Shigi da Fice

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin babban kwanturolan hukumar kula da shigi da fice ta ƙasar, Isah Jere Idris har zuwa ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Buhari ya fitar ta tsawaita wa’adin mai ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatar fadar shugaban Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari.

Wannan ne wa’adi na biyu da aka ƙara wa Jere bayan wanda aka yi masa da farko lokacin da ya yi ritaya shekara guda baya.

A watan nan da muke ciki ne Isah Jere ya samu wata wasiƙa daga ma’aikatar tsaro ta Civil Defence kan cewa ya miƙa ragamar hukumarsu ga wanda ya fi kowa muƙayi kafin 24 ga watan Afrilu, kafin a naɗa wani sabon shugaban.

Rahotanni sun ambato cewa wasu ma’aikata a hukumar sun sha alwashin gudanar da zanga-zanga a ranar Juma’a matuƙar gwamnati ta ƙara tsawaita wa’adin Isah Jere.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here