Yaduwar Korona Karo na Biyu: Shugaba Muhammadu Buhari Zai Gana da Kwamitin PTF

Shugaba Buhari zai gana da kwamitin PTF kan COVID-19 a fadar Shugaban kasa.

Fadar Shugaban kasar ce ta bayyana hakan a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Shugaban PTF kuma babban sakataren tarayya, Boss Mustapha, a ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, ya sanar da wasu takunkumai kan hauhawan cutar.

Biyo bayan tsoron barkewar annobar korona a karo na biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin ganawa da mambobin kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

Legit.ng ta ruwaito cewa fadar Shugaban kasa ce taa sanar da hakan a shafinta na Twitter a ranar Talata, 22 ga watan Disamba.

An tattaro cewa taron, wanda zai gudana a fadar Villa da ke Abuja baya rasa nasaba da hauhawan wadanda suka kamu da cutar a kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here