Femi Falana ya Bukaci Shugaba Buhari ya yi wa Sojojin da Aka Samu da Laifin Bore Afuwa
Femi Falana, babban lauya mai kare hakkin bil-adama ya bukaci Shugaba Buhari ya yi wa sojojin da aka samu da laifin bore afuwa.
Sojojin dai an same su da laifin kin bin umurnin shugabanninsu ne a Maiduguri, jahar Borno inda suke yaki da yan ta’adda.
Sojojin sun yi ikirarin cewa sun yi boren ne ga shugabanninsu saboda rashin isasun makamai da kayan aiki na ba su da shi.
Falana ya ce idan har gwamnatin tarayya da na jahohi za su iya yi wa yan ta’adda afuwa ya kamata sojojin suma a yi musu afuwa.
Legas – Babban lauyan Nigeria mai rajin kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN), ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa sojoji 70 da aka samu da laifin bore afuwa, The Cable ta rawaito.
An samu sojojin da laifin yi wa shugabanninsu bore a Maiduguri, Jahar Borno a shekarar 2014 kuma daga bisani aka yanke musu hukunci.
Da farko an yanke wa sojojin hukuncin kisa amma a 2015, bayan Falana ya rika bibiyar shar’arsu, an sauya hukuncin zuwa daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata na 25 ga watan Agustan 2021, da ya aike wa shugaban kasa, Falana ya ce sojojin kawai sun nemi a basu mukamai da suka dace ne domin yaki da yan ta’addan a arewa maso gabas.
Read Also:
A cewar rahoton na The Cable, Babban lauyan ya ce ba laifin sojojin bane cewa ba a samar musu da makamai da sauran abuwan da suke bukata ba.
Ya ce idan har gwamnati za ta karbar afuwar tubabbun yan ta’adda, sojojin da kawai nema suka yi a wadatar da su kayan aiki suma sun cancanci a yi musu afuwa.
Mene wasikar Falana ta kunsa?
Wani sashi na wasikar ya ce:
“Kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan binciken siyo makamai ya tabbatar da cewa wasu sojoji da farar hula sun karkatar da $2.1 biliyan da N643 biliyan.
Sojojin da suka karkatar da kudaden ne suka yi wa yaki da ta’addancin zagon kasa.”
“Duba da karkatar da kudaden makaman da sojojin da farar hular suka yi, kamata ya yi a tuhume su da bore, zagon kasa da laifukan yaki.Amma saboda rufa-rufa sai tsiraru daga cikinsu ne kawai hukumar EFCC ta tuhuma da karkatar da kudade.
“Har wa yau, Shugaban kasa ya yarda cewa an yi wa sojojin rashin adalci a hirar da BBC Hausa ta wallafa a ranar 28 ga watan Disamban 2015. A lokacin ya ce ‘gwamnain wancan lokacin ta tura sojoji filin daga ba tare da makamai da kayan yaki ba. Wannan shine abin da yasa suke yi boren kuma aka kama su.
“Kowa dai ya sani cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatin jahohi sun yi wa yan ta’addan da suka dauki makami suka yaki Nigeria afuwa. Sojojin da aka yanke wa hukunci saboda sun nemi a basu makamai su yaki yan ta’adda ne suka fi cancantar afuwa daga gwamnatin tarayya.”