Yadda Sabon Jakadan Najeriya, Tukur Buratai ya Taimaka Wajen Kama Sunday Igboho
Tukur Yusuf Buratai ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a garin Cotonou .
Sabon Jakadan Najeriyan ya rubuta takarda zuwa ga Gwamnatin kasar wajen.
Tsohon shugaban hafsun sojan kasan ya na da alaka mai kyau da DSS da NIA Tsohon shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya taimaka wajen cafke Sunday Igboho a Benin.
Crime Channels ta ce Tukur Yusuf Buratai ya bada gudumuwa wajen kama wannan mutumi tare da mai dakinsa, Rapo, a hanyarsu ta zuwa kasar Jamus.
An dade da gane gudun ruwan Igboho Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi da jami’an Najeriya sun dade da gano inda Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya boye.
Read Also:
Jami’an tsaro sun kyale Sunday Igboho ne domin su iya kama shi cikin ruwan sanyi, ba tare da an zubar da jini ba, hakan kuwa aka yi a daren Talatar nan.
A lokacin da Igboho ya samu takardar fasfon bogi, sai gwamnatin tarayya ta kara sa masa ido.
Najeriya ta sanar da kasashen da ta ke makwabtaka da su cewa su yi hattara da Igboho.
A ranar Litinin aka kama shi a filin jirgin Cadjèhoun da ke Cotonou.
Takardar Buratai ta hana Igboho zuwa Jamus Tukur Yusuf Buratai wanda bai dade da zama Jakadan Najeriya a kasar Benin ba, ya rubuta wa gwamnatin kasar Benin takarda a game da wannan mutum.
Buratai ya na aiki ne tare da jami’an tsaron leken asiri na DSS da na harkokin kasashen waje, NIA. Wani jami’in tsaro ya sanar da PRNigeria cewa Janar Buratai (mai ritaya), ya dage a kan sai an kama Igboho, kuma an dawo da shi Najeriya daga Cotonou.
Takardar sabon jakadan ya shiga hannun gwamnatin Benin ne ta ofishin jakadancin Najeriya, wannan ya taimaka sosai wajen hana shi zuwa kasar Jamus.