Wanda ya fi Cancanta ya Gaji Shugaba Buhari a 2023 – Adeseye Ogunlewe
Tsohon minista a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.
Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za’a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jahar Legas.
Yace a halin yanzun babu wanda yafi Tinubu dace wa ya nemi takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin APC.
Lagos – Tsohon ministan ayyuka, Adeseye Ogunlewe, ya yi kira ga jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gaggauta bayyana sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
The cable ta rawaito cewa tsohon ministan na ganin babu wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a 2023 kamar Tinubu.
Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na Arise TV, ranar Talata, Ogunlewe, ya bayyana cewa Tinubu shine wanda ya cancanta ya gaji shugaba Buhari.
Zamu fara yaƙin neman zaɓen Tinubu – Igunlewe
Read Also:
Ya ƙara da cewa, a ranar Alhamis mai zuwa zasu kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu domin nuna goyon baya ga takararsa a zaɓen 2023.
Yace:
“Muna bukatar mutum mai zurfin tunani kuma mutum wanda ya sadaukar da kansa domin cigaban demokaraɗiyya. Saboda haka muna kira ga Sanata Tinubu ya fito ya bayyana.”
“Ba abune mai sauki ba, sai an yi faɗi tashi, kuma sai ya jawo hankalin mutane kan cewa a shirye yake ya musu aiki.”
“Ranar Alhamis zamu kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓensa a reshen jahar Legas domin haka zai nuna wa kowa kudirinsa na neman tikitin takara.”
Shin dagaske Bola Tinubu ba shi da lafiya?
Tsohon ministan ya ƙara da cewa bayan kaddamarwa a Lagos, daga nan za’a matsa zuwa gangamin taron jam’iyya na ƙasa, inda anan za’a zaɓi wannan zai fafata takara karkashin APC.
Ogunlewe ya ƙara da cewa:
“Ba shi da lafiya amma yana samun sauki sosai, yana da isasshen lokacin murmurewa kuma ya dawo ya faɗa mana zai tsaya takara ko a’a.”
“Amma wajibi ya amimce, domin muna tunanin babu wanda ya dace ya jagoranci Najeriya sama da shi.”