Ya Kamata Gwamnatin Tarayya ta Canza Salon da Take Amfani Dashi Wajen Yaƙi da Matsalar Tsaro – Sanata Rochas Okorocha

 

Tsohon gwamnan jahar Imo kuma zaɓaɓɓen sanata a jam’iyyar APC yace sama da kashi 75% na yan Najeriya basa jin daɗin wannan gwamnatin.

Sanata Rochas Okorocha na jahar Imo yace ya kamata gwamnatin tarayya ta canza salon da take amfani dashi wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Sanatan yace amafani da ƙarfin soji kaɗai ba zai warware matsalar tsaron da Najeriya ke fama dashi ba.

Tsohon gwamnan jahar Imo, Sanata Rochas Okorocha (APC, Imo) yace sama da kashi 75% na yan Najeriya suna takaicin abinda ke faruwa a ƙasar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Okorocha ya bayyana hakane a yayin da ya karbi baƙuncin dandazon mabiya addinin musulunci cikinsu harda masu nakasa domin shan ruwa tare ranar Litinin.

Sanatan yace ba yadda za’ai ayi tsammanin abu mai amfani daga wurin mutanen dake cikin takaici da bacin rai.

Okrocha yace:

“Ba zaka iya warware matsala ba sai ka gano tushenta, babban abinda ya jawo wa Najeriya matsalar tsaron da take fama dashi shine rashin adalci da talauci, sai kuma rashin ɗaukar mataki da gwamnati ke yi.”

“Rashin adalci da kuma talauci da yayi wa yan ƙasa katutu shine babban abinda ya jawo mana matsalar tsaron da muke fama dashi.”

“Idan gwamnati na son rage fushin da yan Najeriya ke ciki, to ya zama wajibe da magance rashin adalci tare da yin duk me yuwuwa domin saka al’ummarta cikin farin ciki.”

Sanatan ya roƙi gwamnatin tarayya data canza salonta wajen yaƙi da matsalar tsaro, inda yace amfani da ƙarfin soji kaɗai bazai magance matsalar ba.

Ya kuma shawarci gwamnatin da ta fara tattaunawar neman zaman lafiya kuma ta saka mutane a ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here