An Ceto Jami’in Gwamnatin Jihar Kano Daga Hannun ‘Yan Ta’adda

 

Jami’an tsaron farin kaya ta DSS sun ceto sakataren ƙaramar hukuma da wasu ‘yan ta’adda suka sace daga gidansa a Kano.

Hukumar ta samu nasarar kama matasa biyu daga cikin wadanda ake zargi yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi.

Masu garkuwar sun shiga gidan jami’in gwamnatin ana bikin Sallah, suka sace shi sannan suka nemi kuɗin fansar N300m.

Jihar Kano – Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta samu nasarar ceto sakataren gudanarwa na ƙaramar hukumar Kibiya a jihar Kano, Alhaji Hamza Durya.

Wasu ‘yan ta’adda da suka shiga garin da daddare a lokacin da ake bikin Sallah, suka yi gaba da shi tare da neman fana daga baya.

Daily Trust ta wallafa cewa Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya tabbatar da ceto jami’in.

An ceto jami’in gwamnatin jihar Kano

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa kwamishinan ya bayyana cewa jami’an DSS sun kaddamar da wani samame cikin gaggawa domin ceto jami’in da aka sace a makon jiya.

Ya ce jami’an sun nuna ƙwarewa wajen gudanar da aikin, inda suka kubutar da shi cikin ƙoshin lafiya ba tare da komai ya same shi ba.

Ya kara da bayyana cewa jami’an da suka kaddamar da aikin ceton sun kama mutane biyu da ake zargi, duk da cewa sun samu raunukan harbi yayin artabun.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana wannan nasara a matsayin abin a yaba, tana mai cewa hakan ya nuna jajircewar jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma ta jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf yana ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki da goyon baya domin inganta ayyukansu a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Bukatar gwamnati ga jama’ar Kano

An kuma bukaci al’umma da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu mai kama da shakku ga hukumomi, domin haɗin kai tsakanin jama’a da jami’an tsaro na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da laifuka.

Da yake bayani kan abin da ya faru da shi, Durya ya ce masu garkuwa da mutanen sun fara ne da tayar da ɗansa daga barci, inda suka tilasta masa ya nuna masu inda yake.

Daga nan ne suka daure shi da sarƙa tare da rufe masa ido, suka kai shi wani ɗakin kaji da dabbobi a wani gari da ke kusa a ƙaramar hukumar Rano.

Ya ce a tsawon lokacin da yake hannunsu, ba ya ganin suna yin Sallah, sannan sun riƙa neman kuɗin fansa mai yawa.

A cewarsa, sun fara da neman Naira miliyan 300, daga baya suka rage zuwa miliyan 100, sannan suka sake dagewa kan adadin bayan sun ji cewa yana da kusanci da gwamnan Kano.

Durya ya kuma zargi cewa wani daga cikin makusantansa ne ya ba su bayanai, inda ya yaudare su cewa yana da kuɗi masu yawa.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigan sun fito ne daga Rijana a jihar Kaduna, yana mai godiya ga DSS bisa ceton rayuwarsa ba tare da an biya ko sisi ba.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, mai suna Nasiru, ya amsa cewa sun fito daga Rijana ne domin aikata wannan ta’asa, kuma sun samu taimakon wasu masu ba su bayanai a cikin yankin.

Ya ce su kusan mutum 10 ne, amma yawancinsu sun tsere yayin artabu da jami’an tsaro, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here