Ina Cikin Tasku Saboda Tsadar Dizel – Olusegun Obasanjo

 

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi orafi akan tsadar dizel, da farashin abincin dabbobi da kuma farashin canji da yadda hakan ke shafar noman kifi a Najeriya.

Obasanjo wanda manomin kifi ne ya ce yana cikin tasku saboda tsadar dizel, lamarin da ke kawo tsaiko ga noman kifinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obasanjo ya yi wannan magana ce a jiya Talata a Abeokuta da ke jihar Ogun, a lokacin taron kungiar manoman kifi na yankin kudu maso yammacin Najeria a cikin dakin karatun littafi na Obasanjo (OOPL).

Obasanjo ya bayyana cewa cigaba da tashin farashin dizel da kuma cigaba da karuwar farashin abincin kifi zai hana manoman yin aikinsu, sai dai in har sun hada kai su amince da farashi da zasu cigaba da barin su suna sana’ar.

Ya yi bayani yana cewa a halin yanzu farashin dizel 800 ne lita daya, sannan samar da kilo daya na kifi naira 1,400 ne, kuma ya kara da cewa, idan har suna son samun riba, to ba za su iya sayar da kifi kasa da 1500, lamarin da ya su duk wani abu da ya yi kasa da haka zai jawo faduwa ne da asara.

Obasanjo ya ce: “Farashin dizel ya yi sama saboda yadda ake tafiyar da kasar nan ba yadda ya dace ba ne.

“Saboda haka idan haka ta faru, wasu daga cikin mu da muke bukatar amfani da dizel domin noman kifi zamu yi asarar ne baki daya, kuma a lokacin da hakan zai faru, ‘yan Najeriya za su ci gaba da bukatar cin kifi.”

“Noman kifi zai gagara, sannan manoman da ke wajen Najeriya zasu ringa kawo wa nan.

“Za ka rasa aikin yi, ka talaue. Saboda haka me ya kamata mu yi? Mu hada kai mu cigaba da raya noman kifi domin kula da bukatun wadanda su ke cin kifi da kuma masu noman kifin,” a cewarsa

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here