Gwamna Ganduje ya Bayyana Cin Hanci da Rashawa a Matsayin Abinda ya Hana Kasa Cigaba

 

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ba zai bari a samu cigaba na kwarai a Najeriya ba.

A cewar Ganduje, da irin wannan cin hanci da rashawar da akeyi a Najeriya, da kamar wuya a samu cigaba saboda cin hanci yana kashe kasar.

Ya bayyana hakan ne a zaman kaddamar da wani kwamiti na musamman na dabarun yaki da rashawa a jahar, rahoton BBC Hausa.

“Za ku yarda da ni idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci.

Ba za mu motsa ko ina ba,” in ji Ganduje. An kaddamar da wannan kwamitin ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Afrlu, 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here