Karin Wa’adin Sifeto Janar: Rundunar ‘Yan Sanda ta yi Martani Kan Batun
Rundunar ‘yan sanda ta karyata rahoton da wata kafar yada labarai ta watsa akan IGP Adamu, babban rundunar ‘yan sanda.
Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa IGP Adamu ya bayar da cin hancin N2bn domin a kara masa wa’adi.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba, ya karyata rahoton tare da sanar da cewa IGP Adamu zai nemi hakkinsa a kotu.
Mohammed Adamu, Insifeta Janar na rundunar ƴan sanda (IGP), bai biya N2bn domin a tsawaita wa’adin muƙamin sa na IGP ba, cewar mai magana da yawun rundunar yan sanda na kasa, Frank Mba a ranar Litinin.
Read Also:
Mba ya bayyana cewa shugaban ƙasa ne kawai ya ke da alhakin kara wa’adin muƙamin IGP, kuma shi ɗin ne ya ga dama ya kara ba wai cin hanci ne aka bayar ba, kamar yadda TheCable ta rawaito.
A ranar Litinin ne wa’adin Adamu ya ke karewa tare da yin ritaya daga aiki bayan da ya shafe shekaru 35 yana aikin gwamnati, wannan dai wata doka ce daga cikin kundin mulkin kasar Nigeria na yin ritaya bayan wa’adin aikin shekaru 35.
Sai dai, IGP Adamu ya damu sahalewar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya ci gaba da aiki na tsawon watanni uku nan gaba, inda kuma daga bisani ne rahotanni suka ci gaba da yawo a kafofin sada zumunta na cewar Adamu ya biya cin hanci ne domin a kara wa’adin muƙamin sa.