Bidiyon Tafsirin Pantami: A Cire Tsoro a yi Abinda ya Dace – Aisha Buhari
Uwar gidan shugaba kasa, Aisha Buhari ta caccaki ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami.
Ta bukaci ya ji tsoron Allah ya yi abinda ya dace wa ‘yan kasa yayin da ta yada wani bidiyo nasa.
Ta lika bidiyon malamin kuma minista tare da cewa: ‘A chire tsoro a yi abinda ya dace’ a shafinta na Instagram.
Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari a ranar Lahadi 12 ga watan Satumba ta yada wani bidiyon da ke nuna Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami, yana kuka yayin daya daga cikin wa’azinsa na baya-bayan nan.
Read Also:
Pantami ya kasance mai yawan kuka yayin zaman tafsirinsa lokacin da ake karanta wasu ayoyi a cikin Alƙur’ani Mai Girma, ko lokacin da yake bayanin musgunawa Musulmi.
Aisha Buhari ta yada bidiyon a shafinta na Instagram tare da wata sanarwa mai tsauri: “A cire tsoro a yi abinda ya dace”.
A cikin gajeren bidiyon, Pantami da mai ja masa baki sun fashe da kuka lokacin da ministan ya nemi mai karatun ya karanta wata aya akan tsoron Allah.
Alaramma mai jan baki ya jawo aya ta 63 ta Suratu Maryam, ayar da ke magana kan sakamakon da Allah zai yi wa bayinsa masu tsoron Allah.
Yayin da Pantami ya fara sharhin ayar, shi ma ya fashe da kuka, yana cewa:
“Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu. Ya Allah ka sanya ni daga cikinsu.”