CSOs ta Bayyana Pantami a Matsayin Mutum Mai Nagarta da Basira

 

Hadakar Kungiyoyi Masu Kare Hakkin Bil’Adama, CSOs sun yi kira da Shugaba Buhari ya yi watsi da masu neman a sauke Dr Pantami.

A cewar kungiyoyin, wasu marasa kishin kasa ne da ba su son zaman lafiya da tsaro suka dauki nauyin abin saboda a dakatar da rajistar NIN.

Kungiyoyin sun ce Ministan na Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani mutum ne mai nagarta da ke kawo sauye-sauye masu amfani a kasar.

Hadakar Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’Adama da Tabbatar da Mulki na Gari ta ce wasu ne suka dauki nauyin kiraye-kirayen da ake yi a kafafen sada zumunta na neman sauke Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami da nufin kara lalata harkar tsaro a kasar.

Hadakar ta ce wadanda suka dauki nauyin abin suna cigaba da samun riba daga kallubalen rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassar kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A jawabin da ya yi a Legas a ranar Talata 20 ga watan Afrilu, jagoran hadakar, Kwamared Declan Ihekaire, ya ce sun damu kan ganin yadda ake ci cigaba da neman sai Pantami ya sauka.

Hadakar ta bayyana Pantami a matsayin mutum mai nagarta da basira kuma daga cikin mutane masu muhimmanci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ihekaire ya ce tilas ta sa suka fito domin yin Allah wadai da bata sunan da wasu marasa kishin kasa da ke amfana da rashin tsaro ke yi wa Dr Pantami da masu adawa da batun rajistan NIN wanda zai taimakawa kasar wurin dakile laifuka da samar da tsaro.

Har wa yau, kungiyoyin sun ce sun gamsu da gaskiya irin ta Dr Isa Pantami inda ya amsa cewa a baya ya furta wasu maganganu da ake yi wa kallon goyon bayan kungiyoyin ta’addanci amma tuni girma ya zo masa kuma ya sauya tunaninsa.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da masu kiraye-kirayen ya sauke Dr Pantami kuma kada ya bari marasa kishin kasa su lalata masa gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here