Daga Ƙaramar Hukumar Miga

A ƙoƙarinta na tallafawa al’umma mabuƙata a wannan wata na Ramadan mai albarka, yanzu haka gidauniyar mai girma shugaban hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), (Malam Inuwa Foundation), ta raba tallafin shinkafa (Buhu 100) ga mutane gajiyayyu da masu rauni da gidajen marayu a ƙaramar hukumar Miga, da ke Jihar Jigawa.

Rabon ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Hakimin garin na Miga, Alhaji Sani Yakubu, a fadarsa, da kuma sakataren gidauniyar, Malam Muhammad Dauda Bashir, (Wambai) a yau.

Talata, 5 ga watan Afrelu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here