Sace Mahaifin Kakakinta: An Dakatar da Zaman Majalisa a Jahar Zamfara

 

Majalisar Jahar Zamfara ta dakatar da zamanta saboda sace mahaifin kakakinta.

Yan bindiga sun sace Alhaji Mua’azu Abubakar ne yayin harin da suka kai a garinsu.

Majiya daga majalisar ta ce ba za a cigaba da zaman majalisar ba sai an ceto wadanda aka sacen.

Majalisar Jahar Zamfara ta dakatar da zamanta har sai baba ta gani saboda sace mahaifin kakakin majalisar kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Makonni uku da suka gabata ne yan bindiga suka sace mahaifin kakakin majalisar bayan kai hari a garinsu na Magarya a yankin Kanwa na karamar hukumar Zurmi.

Mahaifin kakakin majalisar da aka sace, Alhaji Mua’azu Abubakar shine hakimin Sabon Garon Magarya a yankin Kanwa a karamar hukumar.

Daily Trust ta rawaito cewa yan bindigan sun kuma sace kishiyoyin mahaifiyar kakakin majalisar yayin da suka kai harin. Kakakin na wakiltar mazabar Zurmi ta Gabas ne a majalisar.

Halin da ake ciki da yan bindigan?

An fara tattaunawa da yan bindigan kuma rahotanni sun ce yan bindigan na ta sauya sharrudan da suka son a cika musu kafin sakin mahaifin kakakin.

Wani shugaban yan bindiga mai suna Halilu Kachalla aka ce shine ke taimakon mahukunta don ganin an ceto mahaifin kakakin da sauran mutanen.

Amma wata kwakwarar majiya ta shaidaw majiyar Legit.ng cewa majalisar na Zamfara ta dakatar da zamanta bayan afkuwar lamarin.

Majiyar, babban jami’i a majalisar, ya ce yan majalisar sun damu matuka da afkuwar lamarin.

Yaushe za a cigaba da zaman majalisar?

Majiyar ya kara da cewa:

“Akwai bututuwa da dama da ke gaban majalisar kaman maganan tantance zababbun kwamishinoni da wasu abubuwan da aka dakatar sai an sako mahaifin kakakin.”

Majiyar ya kara da cewa an mika musu sunayen zababbun kwamishinonin tun makonni biyu da suka gabata amma sun yanke shawarar ba za su duba batun ba sai an ceto wadanda aka sace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here