Dakarun  Operation Hadin Kai Sun Dakile Yunkurin ISWAP na Kai Hari Kan Tubabbun  Ƴan Boko Haram a Damboa

 

Ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP sun yi yunƙurin kai hari a sansanin da aka tanada na musamman na tubabbun ƴan Boko Haram da ke garin Damboa a jahar Yobe. Ƙungiyar ta yi hakan ne domin ta sa tubabbun su karaya. Ƙungiyar kuma ta na baƙin cikin yadda kwamandoji da sauran ƴan ƙungiyar Boko Haram ke miƙa wuya domin rungumar zaman lafiya.

A dalilin haka ne ya sa ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP ta yi yunƙuri a ranar Asabar 2 ga Oktoba, 2021 ta kai hari da kuma kama ƴan ƙungiyar Boko Haram da suka miƙa wuya. Dakarun haɗaɗɗiyar rundunar Birged na 25 wanda ke da makamai masu inganci sun tilastawa ƙungiyar ISWAP janƴewa kuma suka tsere.

Rundunar sojojin ƙasan na tabbatar wa al’ummar garin Damboa da kewaye cewa su ci gaba da harkokin su na yau da kullum. Dakarun za su ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar yankin.

Ana kuma kira gare su da su bayar da muhimman bayanai akan ayyukan waɗannan ƴan ta’adda da masu ɗaukan nauyin su.

Babban hafsan rundunar sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya yabawa dakarun domin hazaƙar su da jajircewa. Ya kuma yi kira a gare su da su bi ƴan ta’addan har maɓoyar su. Ya kuma yi alƙawarin samar da dukkan taimako domin ci gaba da samun nasara a ayyukan Operation HADIN KAI.

 

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu

Daraktan Hulda Jama’a na Rundunar Sojojin Ƙasan Najeriya

3 Oktoba, 2021

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here