Yadda Wasu Daliban Su Tsira a Hannun ‘Yan Bindiga
Rahotanni da sanyin safiyar ranar Asabar sun wallafa labarin yadda ‘yan bindiga suka kai hari wata makarantar sakandire a Katsina.
‘Yan bindiga sun dira dakin kwanan dalibai da ke makarantar sakandiren kimiyya a Kankara tare da yin awon gaba da dalibai.
A yayin da rahotanni suka bayyana cewa wasu daga cikin daliban sun dawo, har yanzu da dama sun bace
Har yanzu fiye da dalibai 300 ne ake zargin cewa su na hannun ‘yan bindigar da suka shiga cikin dakunansu na kwana, a makarantar sakandiren kimiyyya da ke Kankara, su ka yi awon gaba da su, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Read Also:
TheCable ta yi ikirarin cewa majiyar jami’an ta sanar da ita cewa har ya zuwa yammacin ranar Asabar ba’a san makomar dalibai 345 ba, ba’a san inda suke ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara, jihar Katsina, da talatainin daren Juma’a zuwa duku-dukun safiyar Asabar, tare da yin awon gaba da dalibai kusan 600.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa akwai kimanin dalibai 800 a cikin makarantar, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin, amma wasu daga cikinsu sun samu damar sulalewa ta hanyar tsallaka katangar makaranta.
Yan bindigar sun harbe wani maigadi da ke kula da tsaron harabar makarantar. A ranar Asabar ne rundunar ‘yan sanda ta sanar da cewa an samu kimanin dalibai 200 da suka dawo daga baya.
Isah Gambo, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ya sanar da cewa tuni an fara bincike da bin sahu domin gano dukkan sauran daliban da har yanzu ba’a san inda suke ba tun bayan harin ‘yan bindigar.