Daliban da Akai Garkuwa Dasu na ABU Sun Samu Yanci

Daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya su tara da aka yi garkuwa da su, sun samu yancinsu.

Shugaban tsaro na jami’ar ya tabbatar da hakan sai dai ya ce yana jiran samun cikakken bayani daga wani shugaba na sashin harshen Faransa da ke makarantar.

Hakazalika wani mutum da ya yi ikirarin kasancewa yayan daya daga cikin daliban da aka sace, ya ce an sako kanwar tasa.

Rahotanni sun kawo cewa an saki daliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna su tara da aka yi garkuwa da su.

An yi garkuwa da su ne a wani hari da aka kai wa masu motoci a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Dickson Oko, daya daga cikin daliban wanda ya tsere amma ya samu rauni sakamakon harbin bindiga, ya ce dama masu garkuwan sun tuntubi iyalan daliban sannan suka bukaci naira miliyan 30 kafin a saki kowannensu.

Akwai rahotannin cewa masu garkuwa da mutanen sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan daya kowani dalibi.

Da yake zantawa da jaridar TheCable a ranar Lahadi, Ashiru Zango, Shugaban tsaro na ABU, ya ce sun samu bayanin cewa an sake su amma dai har yanzu suna jiran cikakken bayani daga Shugaban bangaren harshen Faransa.

Rahoton ya nuna cewa Zango ya bukaci a kara tuntubarsa a nan gaba. “Har yanzu ina jiran cikakken bayani daga Shugaban bangaren (Faransa).

“Amma wani ya fada mani cewa an sake su,” in ji shi. Bugu da kari, wani mai suna Julius Mutum wandda ya bayyana cewa shi dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace, ya wallafa a shafin Twitter cewa an saki yar’uwarsa.

“Wasu daga cikin yan ABU 9 ciki harda kanwarta sun samu yancinsu. Yan uwa ne suka yi fafutukar.

Muna godiya @TheAbusite a kan daga muryoyinku da kuka yi a lokacin da gwamnati da jami’an tsaro suka ki yin komai,” ya wallafa.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa miyagu sun nemi a biya Naira miliyan 270 kafin su fito da wadannan ‘dalibai har tara da su ka tsare.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here