Yadda daliget ya Raba wa Jama’ar Karamar Hukumarsa N7m da ya Samo a Zaɓen Fitar da Gwani na PDP
Wani daliget na jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, wanda ya samu kuɗi lokacin zaɓen fitar da gwani, ya raba kudin ga jama’ar karamar hukumarsa ta Sanga da ke Jihar Kaduna.
Mutumin mai suna Tanko Rossi Sabo ya wallafa a shafinsa na Facebook yadda ya raba wa mabuƙata miliyoyin kuɗi bayan ya koma gida.
An yi zargin cewa wasu masu neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP sun raba maƙudan kuɗaɗe da suka hada da dalar Amurka ga daliget domin su zaɓe su.
Sai dai jam’iyyar ta PDP ta musanta zargin.
Lamarin ya sa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta aike da jami’anta filin zaben fitar da gwanin inda aka gan su suna sanya ido kan abubuwan da ke wakana a dandalin.
Akwai rahotanni daban-daban kan adadin kuɗaɗen da ya samu, inda wasu ke cewa sun kai naira miliyan 12, sai dai hotunan da ya wallafa sun nuna ya raba kusan naira miliyan bakwai.
Read Also:
BBC Hausa ta yunƙurin ji daga bakin honorabul ɗin amma wayoyinsa ba sa shiga ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Abin da aka yi da kuɗin da honorabul Tanko ya bayar
Ɗan jarida kuma tsohon mai ba wa tsohon Gwamnan Kaduna Ibrahim Yakowa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Rueben Buhari, ya faɗa BBC Hausa cewa da ma tun kafin ya zama daliget Tanko ya yi wa jama’ar mazaɓarsa alƙawari.
“Da ma tun lokacin da yake takara ya faɗa wa ‘yan mazaɓarsa cewa idan suka zaɓe shi a matsayin daliget na ƙasa zai kawo duk abin da ya samu a raba,” in ji Rueben.
Abubuwan da aka yi da kuɗin sun haɗa da sayen rigunan ƙwallon ƙafa da biyan kuɗin makaranta da asibiti ga mutane. Ya kuma raba sauran kuɗaɗen ga magoya bayansa.
Mista Tanko ya ce ko wacce irin muhawara ko suka da za a tafka bai dame shi ba, tunda dai duk abin da ya samo ya dawo gida ya sanya farin ciki a fuskokin al’ummarsa.
Tanko Rossi na cikin delegates din Kaduna da suka halarci taron PDP na kasa inda aka gudanar da zabe da tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takara a PDP.