Dalilan da Yasa Kotun Koli ta Soke Jam’iyyun Siyasa 74
Bayan shekara daya ana fafatawa a kotu, abin ya zo karshe.
Kotun Koli ta rraba gardama tsakanin INEC da jam’iyyun siyasa 74 da aka soke.
Kotun ta ce hukumar INEC na da karfin soke jam’iyyun siyasa a doka.
Kotun kolin Najeriya a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara inda aka amince da INEC ta soke jam’iyyar siyasa 74 saboda basu ci zabe ko guda ba.
A bara Legit ta kawo muku cewa, hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74 a Najeriya.
Jam’iyyun da suka rage yanzu 16 ne kacal.
A zaman yanke hukuncin da Alkali Adamu Jauro ya jagoranta ranar Juma’a a Kotun Koli, ya ce soke jam’iyyar NUP da sauran jam’iyyu 73 daidai ne da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana dalilan da yasa aka soke jam’iyyun.
Dalilan sune:
Read Also:
1. Saba dokokin rijistan jam’iyyar siyasa a Najeriya
2. Gaza samun 25% na kuri’u a jaha ko daya a zaben shugaban kasa da ya gabata, sannan gaza samun 25% na kuri’u a karamar hukuma ko daya a zaben gwamnonin jahohi 36
3. Gaza cin zabe a yanki daya a zaben shugaban karamar hukuma a kananan hukumomi 774, gaza cin kujerar dan majalisa daya a jahohin Najeriya da gaza cin kujeran kansila ko daya a fadin tarayya
Jam’iyyun da suka rage sune:
Jam’iyyar Accord
Jam’iyyar Action Alliance AA
Jam’iyyar African Action Congress AAC
Jam’iyyar ADC
Jam’iyyar APC
Jam’iyyar ADP
Jam’iyyar APGA
Jam’iyyar APM
Jam’iyyar LP
Jam’iyyar NNPP
Jam’iyyar NRM
Jam’iyyar PDP
Jam’iyyar PRP
Jam’iyyar SDP
Jam’iyyar YPP
Jam’iyyar ZLP
Jam’iyyar BP
Jam’iyyar APP