Dalilin da Yasa na Biyawa Dalibai 2000 Kudin Jarabawar NECO da NBAIS – Jibrin Kofa
Abdulmumin Jibrin ya dauki nauyi dalibai 2000 domin su rubuta jarabawar NECO da NBAIS
Tsohon dan majalisar wakilai ta kasa Honourable Abdulmumin Jibrin Kofa ya biyawa yara dubu biyu wadanda bazasu iya biyan kudin jarabawar NECO da NBAIS ta shekarar 2021 naira 11,500 kowannen su domin su rubuta jarabawar.
A yayin da yake jawabi ga daliban a garinsa dake Kofa a karamar hukumar Bebeji Hon. Jibrin ya bayyana cewar ya biyawa daliban kudin jarabawar ne a matsayin gudummawar sa ga bangaran ilimi wanda yanada matukar alfanu a bangarori da dama musamman akan shaanin tsaro.
Read Also:
Jibrin wanda babban daraka ne a shaanin kasuwanci na hukumar gidaje ta kasa yace dukda cewa gwamnatin jiha ta bada tata gudummawar wajen daukar nauyin dalibai, “yana da kyau muma mu kara a matsayin tamu gudummawar wajen taimakawa gwamnatin Shugaba Buhari da gwamna Ganduje a nan kano.
“Ina so in saka muku kaimi domin ku sake dage damtse wajen neman ilimi, wadanda bazasu iya biyawa kansu kudin wannan jarabawa ta NECO da NBAIS sun samu wannan dama a yau.
Bama so mu ganku kuna yawo a titi, wannan dawainiyya ce akan duk wani dan Najeriya wajen ganin rayuwar mutane ta inganta”.
Sannan ya sake kira ga daliban da suka samu wannan dama dasuyi amfani da ita domin samun gobe me kyau.
Taron ya samu halartar shugabannin dalibai, shugabannin alumma, na jamiyya da kuma masu ruwa da tsaki a fannoni da dama.