Wata Majiya: Dalilin Kashe Manoman Shinkafa
Majiya ta bayyana dalilin da yasa mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa manoma yankan rago a garin Zabarmari da ke jihar Borno.
An tattaro cewa mazauna kauyen sun kama daya daga cikin yan ta’addan a yayinda suka je neman abinci da kayan amfani har suka mika shi ga sojoji.
Wannan jarumta na mazauna yankin ne ya tunzura yan ta’addan har suka far masu a ranar Asabar a lokacin da suke gona.
Rahotanni sun kawo cewa Zabarmari ta shiga matsala ne a tsakanin ranakun Alhamis da Juma’a, lokacin da mayakan Boko Haram masu biyayya ga Abubakar Shekau suka je garin domin farautar abinci da sauran kayayyakin bukata daga mazauna yankin.
“Bibiyar mazauna kauye da bindiga don samun abinci, kudi da sauran kayayyakin amfani na daya daga cikin ayyukan yan ta’addan,” in ji majiya da ke da masaniya a kan abunda ya faru.
Read Also:
“Sai dai a wannan rana ta cika da wani dan ta’adda da ya je Zabarmari a ranar Juma’a sannan ya bukaci wasu iyalai su dafa mashi abinci domin ya kai wa mukarrabansa.
“Sai suka amince amma da ya shiga bayi, sai mazauna kauyen suka tattaro jarumta, suka kwace bindigarsa sannan suka kama shi a lokacin da ya fito.Daga bisani sai suka mika shi ga jami’an tsaro,” in ji majiyar.
Wata majiyar ta ce wannan jarumta da mazauna kauyen suka yi shine ya tunzura yan ta’addan wadanda suka taru bayan sa’o’i 24 sannan suka far ma manoman da ke aiki a kan gonakin shinkafa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Daga nan sai aka dunga kiransu mutum bibbiyu da uku-uku. Mayakan sukan yi masu wasu tambayoyi sannan daga bisani sai su daure hannayensu a bayansu sannan su yi masu yankan rago.
“An fillewa wasu mazauna yankin wuya sannan aka daura kawunan a jikinsu. Wannan shine karshen zalunci saboda yan tsiraru da aka kama ne aka saki a yayin kisan kiyashin,” in ji majiyar.