Gwamnatin Jahar Kogi ta Bayyana Dalilin Tashin Gobara a Makarantar Sakandare da ke Jahar

 

Gwamnatin jahar Kogi ta karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa makiyaya ne suka kona makarantar sakandare ta Iluke Bunu.

Sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jahar, Kingsley Fanwo ya fitar ta ce binciken da aka fara ya nuna kona daji ne ya yi sanadin gobarar.

Fanwo ya ce hukumomin tsaro na cigaba da zurfafa bincike don haka ya yi gargadi kan yadda jita jitar da ka iya tada zaune tsaye a jahar.

Gwamnatin jihar Kogi ta karyata rahotannin da ke cewa makiyaya Fulani ne suka kona makarantar sakandare ta Illuke Bunu inda ta ce kona daji ba bisa ka’ida bane ya janyo gobarar, Vanguard ta ruwaito.

Hakan ne kunshe ne cikin sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jahar, Mista Kingsley Fanwo ya fitar mai taken, ‘Rahoton farko game da kona makarantar sakandare ta Iluke Bunu.’

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin za ta cigaba da zurfafa bincike yayin da ta yi tir da wadanda ke gaggawar alakanta lamarin da wani sashi na al’umma.

“Konewar makarantar sakandare ta Iluke Bunu abu ne da gwamnati ta damu da shi.

“Gwamnatin jahar tana tir da gaggawan da wasu suka yi na cewa makiyaya Fulani ne suka kona wani sashi na makarantar.Irin wannan rahoton mara tabbas na iya tada tarzoma a jahar.

“Binciken da muka fara gudanarwa ya nuna cewa kona daji ba bisa ka’ida ba da wasu mutane biyu da ba a gano su ba suke yi ne ya janyo gobarar.

“A yayin da muke cigaba da bincike kan sababin gobarar, muna gargadi game da yin kalaman da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar da ake yi tsakanin kabiloli a jahar Kogi.

“Al’ummar Kogi suna zaman lafiya da Fulani, Bassa, Nupawa da sauran mutane da ke zaune ko yin kasuwanci a jahar,” a cewar wani sashi na sanarwar.

Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha da Shugaban karamar hukumar Kabba/Bunu da mai bada shawarar kan tsaro na jahar sun bukaci hukumomin tsaro su binciko wadanda suka aikata abin don fuskantar sharia.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here