Ɗan bindiga ya Hallaka Mutane 4 a Amurka

A wani sabon tashin hankalin da ya sake afkawa Amurka, wani ɗan bindiga ya kashe aƙalla mutum hudu, a wani asibitin da ke jami’a a birnin Talsa.

Mataimakin shugaban ‘yan sanda Eric Dalg-lish ya ce jami’ansu sun garzaya wurin lokacin da lamarin ya faru.

Ya ce ɗan bindigar ya kashe kan shi, kawo yanzu jami’ansu ba su yi ƙarin haske ba. Amma mu na zaton ya kashe kan shi ne.

Harin na zuwa ne bayan fara jana’izar daliban nan 19 da malamansu biyu da wani ɗan bindiga ya hallaka a Texas a makon jiya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here