Dangote ya Hada N380.38bn a Cikin Watanni 3

Tun daga watan Fabrairu, duniya ta shiga gunaguni game da mamayar Rasha a kasar Ukraine, lamarin da ya jefa miliyoyin ‘yan Ukraine cikin mawuyacin hali.

Sai dai bisa ga dukkan alamu ba ‘yan kasar Ukraine ne kadai ke kage ba, domin kuwa hudu daga cikin attajiran Rasha sun rasa mukaminsu a jerin attajirai, Aliko Dangote ya haura.

Dangote, wanda a farkon 2022 ke cikin mutane 100 mafi arziki da ke raye a duniya, ya tsallake matsayi 21 kuma a yanzu ya zama na 79 a duniya.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yanzu ya fi kusan dukkan attajiran kasar Rasha, banda hudu daga cikinsu.

A cewar jadawalin Bloomberg Billionaires Index, bakar fatar da ya fi kowa kudi a duniya a yanzu yana da kimanin dala biliyan 20 bayan da ya samu sama da dala miliyan 915 (N380.38bn) cikin watanni uku kacal.

Sabon kari na arzikin da ya samu na nuni da cewa Aliko Dangote ya zama attajiri na 79 a raye a duniya.

Shigar Dangote 2022

Dangote dai bai shiga 2022 da kafar dama, domin kuwa ya yi asarar dala miliyan 244 a rana guda bayan kare 2021 a wani matsayi mai inganci.

Dan kasuwan ya fado zuwa na 100 a jerin masu kudin duniya, inda ya mallaki dala biliyan 19.1 kacal.

Sai dai kuma labarin ya sauya sosai bayan ‘yan makonni kadan, kamar yadda a karshen watan Janairun 2022 ya nuna, Dangote ya hau matsayi na 91 a jerin attajiran duniya da zunzurutun kud akalla dala biliyan 19.5.

Haka dai ya ci gaba da habaka a Fabrairu 2022 kuma ya kare watan da zunzurutun dukiyar da ta kai dala biliyan 20.0 yayin da kuma ya yi tsalle ya zuwa matsayi na 84.

A baya-bayan nan a cikin Maris ya hau daya daga cikin mafi girman matakin da ya taba kasancewa.

Rushewar arzikin attajiran Rasha ya taimaka wa habakar Dangote

Faduwar hamshakan attajiran kasar Rasha ne ya kuma taimaka wa Dangote wajen samun nasarar tsallaka matakai a jerin attajiran duniya.

Lokacin da aka shiga 2022, akwai wasu hamshakan attajiran Rasha bakwai da suka dara Dangote arziki.

Sun hada da:

1. Leonid Mikelson

2. Vladimir Potanin

3. Alexei Mordashov

4. Vladimir Lisin

5. Vagit Alekperov

6. Gennady Timchenko

7. Alisher Usmanov

Ya zuwa karshen Maris 2022, Dangote yanzu ya fi dukkan hamshakan attajiran na kasar Rasha arziki idan aka cire Vladimir Potanin, Leonid Mikhelson, Alexey Mordashov da Vladimir Lisin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here