Allah ya yi wa Gogaggen ‘Dan Jarida, Abdulhamid Agaka Rasuwa
Jihar Kaduna – Gogaggen dan jarida kuma kwararre a bangaren kafar watsa labarai, Mallam Abdulhamid Agaka, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton Leadership.
A cewar kafar watsa labarai ta PRNigeria, dan jaridar wanda matarsa da mutu a makon da wuce, ya mutu cikin barcinsa a daren ranar Laraba a gidansa da ke Kaduna.
Takaitaccen tarihin Mallam Abdulhamid
An haife shi a ranar 26 ga watan Fabrairun 1956, Malam Babatunde Agaka ya yi karatun firamari a Capital School Kaduna, kafin ya tafi Kwallejin Barewa da ke Zaria, duk a Kaduna ya kuma tafi Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ilorin, Jihar Kwara.
Ya fara aiki da jaridar New Nigerian, jaridar farko a arewa da ke Kaduna a shekarar 1974.
Read Also:
Daga baya, ya koma tsohuwar jaridar Democrat Newspaper a matsayin Edita daga 1988 zuwa 1997, sannan ya koma aikin bada shawarwari kan kafar watsa labarai. Malam Babatunde Agaka, wanda ya hallarci tarurukan horaswa da karin ilimi masu yawa a gida da waje, mamba ne na Cibiyar aikin jarida ta Najeriya, NIJ, a Legas.
An tattaro kuma cewa ya rike mukamai a kungiyar editoci ta Najeriya, NGE, inda ya ke mamba.
Yaya da yan uwa da marigayin ya bari
Malam Babatunde Agaka, wanda ya taba rike mukamin sakatare na Kwamitin Jokolo da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kafa a 1999, ya bar yara hudu: Ahmad, Maryam, Halima da Abdulhamid (Jnr).
Ya kuma bar yan uwa da suka hada da Mallam Ismail Ila Agaka, tsohon manajan direkta na ‘Nigeria Social Infrastructure Trust Fund, NSITF, da Ilyasu Baba Agaka, direkta a fadar shugaban kasa da wasu.
Dakaci karin bayani …