Mista Ossy Prestige: ALLAH ya yi wa Dan Majalisar Wakilai na Tarayya Rasuwa

 

Dan majalisar wakilai na tarayya, Mista Ossy Prestige ya riga mu gidan gaskiya.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Aba North/South daga jahar Abia.

Ya rasu ne bayan ya dade yana fama da rashin lafiya kamar yadda wata majiya daga iyalansa ta tabbatar Dan majalisar tarayyar Nigeria mai wakiltar jahar Abia, Ossy Prestige ya riga mu gidan gaskiya, Premium Times ta ruwaito.

Dan majalisar mai wakiltar, Aba North/South na jahar Abia ya rasu ne bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

An zabe shi ne a karkashin jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA).

Mai magana da yawunsa, Benjamin Kalu, shima ya tabbatar ta rasuwar dan majalisar cikin sakon kar ta kwana daya aike wa majiyar Legit.ng.

“Wani daga cikin iyalansa ya tabbatar da rasuwarsa,” in ji shi.

tara majiyar, daga shugabannin majalisar wakilai na tarayya ita ma ta tabbatar da rasuwarsa.

“Eh, da gaske ne ya rasu. Za a sanar yayin zaman majalisar gobe sannan a tashi daga zaman,” in ji dan majalisar da ya nemi a sakaya sunansa domin ba a bashi izinin magana kan batun ba.

Marigayi Mista Prestige shine dan majalisar wakilai na tarayya na uku da ya rasu a majalisa zubi ta tara.

Sauran biyun da suka rasu kafin shi sune Ja’afaru Iliyasu da Mohammed Faggen-Gawo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here