2020: Dalilin da Yasa Wani Dan Sanda ya Zama Gwarzon Jami’i
Shahrarren dan sanda wanda ake ikirarin bai taba karban cin hanci ba shekaransa 30 yana aiki, CSP Francis Erhabor, ya zama ‘Jami’in dan sandan shekara’ a zaben lambar yabon Igbere TV 2020.
Erhabor, wanda yake DPO na D Division, Itam, Uyo, jihr Akwa Ibom, ya lallasa wasu hazikan yan sanda biyar a zaben da aka yi.
Sauran jami’an sune, Frank Mba, Olushola Oyebade, Abba Kyari da Aisha Abubakar.
Yan Najeriya ne suka kada kuri’ar ta yanar gizo.
Wannan lambar yabo na Igebere TV yana karrama mutanen da suka fice a wuraren aikinsu.
Za’a yi bikin mika masa lambar yabonsa ranar 10 ga Disamba, 2020, Vanguard ta ruwaito.
Read Also:
Yan Najeriya sun zabi CSP Erhabor ne saboda jajircewarsa da gaskiyansa.
Misali, inda yake jagoranta, beli kyauta ne kuma babu jami’in dan sandan da ya isa ya karbi cin hanci daga hannun mutan gari.
Hakan ya sa mutan garin aminta da yan sanda kuma suna basu goyon baya da taimako idan suka bukata.
Dalilin cikin abubuwa ban al’ajabin da yayi sune:
1. Lokacin da yake kwamandan tsare bututun mai a Edo, ya ki karban cin hancin N1.5m da wasu mutane masu fasa bututun mai suka bukaci bashi kowani mako.
2. Ya ki karban N500,000 a kowani mako da abokan aikinsa suke bashi bayan sun karba cin hanci da rashawa daga wajen masu shigo da jabun man fetur cikin jihar.
Ya ki karban wadannan kudade duk da cewa kudin alawus dinsa N37,500 ne a wata kuma ba ko yaushe yake samu ba.