Mayar da Dala 800: ‘Dan Sanda Ya Samu Kyautar N250,000 da Kujerar Aikin Hajji

 

Wata jarida ta yanar gizo mai suna Katsina City News ta yiwa wani dansanda kyautar Naira 250,000 mayar da Dala 800 da ya tsinta ga mai shi.

Nura Mande da ya dawo dala 800 kudin guzurin tafiyar aikin hajji da wata hajia daga jihar Katsina ta batar a sansanin alhazai.

Hon, Ali Abu Albaba, a lokacin da yake gabatar da kyautar kudi ga Nura Mande ya ce ba kowa bane zai tsinci makudan kudi ya maida wa mai shi su ba.

Jihar Katsina – A ranar Alhamis ne wata jarida ta yanar gizo mai suna Katsina City News ta yiwa wani dansanda kyautar Naira 250,000 da kujerar aikin Hajji saboda ya mayar da Dala 800 da ya tsinta da wata maniyyaciya ta batar. Rahoton Daily Nigeria.

Dan sanda Najeriya mai suna Nura Mande da ya dawo dala 800 kudin guzurin tafiya da wata hajia ta batar a sansanin alhazai na Jihar Katsina gabanin tafiyar ta aikin hajjin bana da ya gabata.

Dan Majalisar Dokokin daga jihar Katsina, Honorable Ali Abu Albaba ne ya jagoranci gabatar da kyautar ga Nura Mande a madadin mawallafin jaridar Katsina City News a Hedikwatar yan Sandan jihar.

Honorable Abu-Albaba ya ce jaridar ta dauki nauyin yiwa Abun Mande kyautar ne saboda gaskiya da tausayi da ya nuna.

Abu Albaba ya kara da cewa ba kowa ne zai tsinci makudan kudi da babu wanda ya gan shi ya mayar wa da mai shi su ba kamar yadda Aminiya ta rawaito.

Dan Majalissar ya ce bayan tukwicin da dan sandan ya samu, daga gidan jarida an kara samu wanda ya shi kyautar kujerar Hajji don sauke farali a shekara mai zuwa.

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here