Yadda Wani Dan Ta’adda ya Kashe Uba da Dan sa

A ranar Litinin da daddare wani dan ta’adda ya je har gidan wani Malam Nuhu ya kashe shi a jihar Kano.

Bayan faruwar lamarin ne dan sa ya bi mutumin da gudu don ya kama sa, amma mutumin yayi ta sharba masa wuka har sai da shima ya mutu.

Al’amarin ya faru ne a kauyen Tumfafi da ke karamar hukumar Garko a jihar Kano, wanda yayi sanadiyyar mutuwar da da uba.

A ranar Litinin, wani dan ta’adda ya kai wa wani Malam Nuhu mazaunin kauyen Tumfafi da ke karamar hukumar Garko da ke jihar Kano, hari, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda masu gani da ido suka ce, dan ta’addan yayi yunkurin kashe Nuhu a gidansa kwanakin baya, har yana sharba masa wuka a hannu.

An ce mutumin ya tsere ne bayan ya kashe Malam Nuhu, bayan ganin hakan ne yasa dan Nuhu ya bi mutumin waje da gudu don ya kama shi.

Sai dai mutumin ya mamayeshi, inda yayi ta datsarsa da wuka a jiki, har sai da ya kashe shi.

Ganau sun shaida yadda aka birne gawar Nuhu da ta dansa da misalin karfe 9 na safe, cikin matsanancin tashin hankali a kauyen Tumfafi.

Har yanzu ba a samu zantawa da jami’in hulda da jama’a ba na ‘yan andan jihar ba, DSP Abdullahi Haruna, don an yi ta nemansa ta wayarsa amma abin ya ci tura.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here