Dakatarwa: Mun Fara Daukar Matakai Don Cika Sharuddan da NCAA ta Gindaya – Kamfanin Jiragen Azman

Kwamitin binciken NCAA ya bayyana dalilin dakatar da jiragen Azman tare da shimfida musu ka’idoji.

Hukumar NCAA dai ta dakatar da Azman Air saboda karya wasu dokokin aiki da kuma tantance ingancin jiragen kamfanin.

Mai magana da yawun kamfanin Azman ya ce za su cika ka’idojin cikin mako guda don tabbatar da jiragen sun dawo aiki ba da jimawa ba.

Hukumar kula da sauka da tashin jiragen sama na kasa (NCAA) ta bayyana dalilan dakatar da jiragen Azman tare da bayyana wasu ka’idoji da za a cika kafin jiragen su dawo aiki, rahoton Daily Trust.

Tuni kamfanin suka fara yunkurin shawo kan matsalolin da aka bayyana da taimakon sashen kula da jirage.

NCAA dai ta dakatar da ayyukan Azman Air saboda dalilin rashin inganci.

A wata samfurin dakata da kwamitin bincike na NCAA wanda wakilinmu ya gani ranar Lahadi ta nuna cewa, an dakatar da jirgin ranar 15 ga watan Maris 2021 bisa rashin cika wasu matakan kariya da hukumar ta shimfida.

Rahoton binciken mai shafi 19 na dauke da sa hannun babban daraktan hukumar NCAA Captain Nuhu Musa dauke da kwanan wata 2 ga Afrilu, 2021. Ana zargin Azman da karya tarin dokoki da suka saba da kundin dokokin hukumar na shekarar 2006.

Amma kamfanin sun ce suna daukar duk wani mataki don shawo kan matsalar.

Bayan sauke shuganban sashen gyare gyare, sun kuma ware bangaren kiyayewa da tabbatar da inganci wanda da a hade suke, kuma suna neman sabon mai kula da sashen kiyayewa.

Mai magana da yawun kamfanin, Mr Nura Aliyu, wanda ya zanta da wakilan Daily Trust daren da ya gabata, ya ce: “mun fara daukar matakai don cika sharuddan.”

Ya tabbatar da cewa duk sharuddan da NCAA ta gindaya za a cika su cikin mako guda don tabbatar da cewa jiragen sun dawo aiki ba da jimawa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here