Na ɗaura ɗamarar Fara Yaƙin Neman Zaɓe Domin Tabbatar da Karɓe Ragamar Najeriya a 2023 – Atiku

Ɗan takarar shugaban kasa a ƙarkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ya ɗaura ɗamarar fara yaƙin neman zaɓe domin tabbatar da karɓe ragamar Najeriya a 2023, da kuma ceto ƙasar daga rashin iya mulki irin na APC cikin shekaru bakwai.

Ɗan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta mika wa Atiku Abubakar shaidar zama ɗan takarar ta a zaɓe mai zuwa.

Ya kuma jaddada amfanin haɗin kai da aiki tuƙuru da kowanne ɗan kasa wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

Yana mai cewa akwai ayyuka da dama kuma lokacinsu na kurewa don haka dole a nuna jajircewa

An zaɓi Atiku Abubakar ne a zaben fitar da gwamni na PDP da aka gudanar a ranar Asabar din ƙarshen mako.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here