DHQ ta Musanta Naɗa Muƙaddashin Hafsun Soji

 

FCT, Abuja – Hedikwatar tsaro ta (DHQ) ta yi magana kan batun naɗa muƙaddashin hafsan sojojin Najeriya (COAS).

DHQ ta sanar da cewa ba ta naɗa wanda zai zama COAS yayin da Taoreed Lagbaja ya tafi hutu ba.

DHQ ta musanta naɗa muƙaddashin hafsun soji

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya fitar a ranar Litinin a shafin X na DHQ.

Tukur Gusau ya ce babu irin wannan naɗin a cikin rundunar sojojin Najeriya, yana mai cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya yi magana da Taoreed Lagbaja ƴan mintuna kaɗan da suka gabata.

A cewarsa, hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, a halin yanzu ya tafi hutu ne.

Ya bayyana cewa ana tafiyar da rundunonin sojoji cikin ƙwarewa, ya ƙara da cewa dukkanin hafsoshin tsaro na gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.

Birgediya Janar Tukur Gusau ya fayyace cewa Manjo Janar Abdulsalam Ibrahim, wanda shi ne shugaban sashen tsare-tsare, ya na ba da bayanai ga Lagbaja kan ayyukan rundunar na yau da kullum.

DHQ ta yi wa jama’a gargaɗi

“DHQ ta buƙaci mutanen da ke yaɗa jita-jita marasa tushe da su daina yin hakan nan take.

“COAS yana cikin ƙoshin lafiya kuma nan ba da jimawa ba zai dawo bakin aiki bayan ya kammala hutunsa.”

– Birgediya Janar Tukur Gusau

Kakakin na DHQ ya gargaɗi masu kiran sojoji su ƙwace mulki su sani cewa irin waɗannan ayyukan cin amanar ƙasa ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin ƙasar nan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here