Direban da ya Kade Jami’in Karota Har Lahira a Jahar Kano ya Gudu

 

Wani direba wanda ba a san ko waye ba ya kade jami’in KAROTA a jahar Kano tare da tserewa kuma ba a kama shi ba.

Kamar yadda aka tattaro, ya banke jami’in ne titin jami’ar Bayero da ke tsakiyar birnin Kano kuma ya gudu.

Kakakin hukumar KAROTA ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce an mika gawar asibitin Murtala.

Wani direba da ba a san ko waye ba a jahar Kano ya banke tare da kashe jami’in hukumar kula da lamurran tituna, KAROTA da ke titin BUK a tsakiyar birnin Kano.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, direban ya tsere bayan ya banke jami’in KAROTA kuma abokan aikinsa sun yi kokarin cafkarsa amma abun ya gagara.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun KAROTA, Nabilusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an mika gawar jami’in asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Abubakar ya ce ba zai iya kara cewa komai ba game da lamarin saboda hukumar na jiran rahoton aukuwar lamarin ne daga asibitin, Daily Nigerian ta rawaito.

Ya kara da daukan alkawarin samar da karin bayani bayan an kammala bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here