Hadiza Bala Usman: ‘Yan Majalisa Sun Bukaci Hukumar EFCC da ta yi Bincike a Kan Hukumar NPA

 

‘Yan adawa a Majalisa sun bukaci ayi cikakken bincike a kan Hukumar NPA.

Hon. Ndudi Elumelu ya ce dakatar da Hadiza Bala Usman da aka yi, bai isa ba.

‘Yan Majalisar suna zargin Ministan sufuri da kokarin lullube badakalar APC.

Marasa rinaye a majalisar wakilan tarayya sun yi kira ga EFCC da sauran hukumomi da su ke da alhakin kama marasa gaskiya su yi bincike a kan aikin NPA.

‘Yan majalisar suna so a bibiyi zargin da ake yi na cewa hukumar NPA mai kula da tashoshin ruwan kasa ba ta dawo da N165bn cikin lalitar gwamnati ba.

Shugaban marasa rinaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu, ya fitar da jawabi inda ya ce bai kamata a ce kwamiti ne kawai zai binciki wadannan zargin ba.

Daiy Trust ta rahoto Honarabul Ndudi Elumelu ya na cewa zargin laifi mai nauyi irin wannan, ya na bukatar EFCC ta gudanar da binciken babu sani, babu sabo.

‘Yan majalisar hamayyar sun ce sun damu da yadda aka bar binciken zargin badakalar da ake tafka wa a hukumar NPA a hannun kwamitin je-ka-na-yi-ka.

“Siyasa ta shiga cikin binciken da ya kamata a gudanar domin a bankado mahukaciyar sata.”

Elumelu ya ce: “Muna zargin cewa zallar dakatarwar da aka yi wa shugabar NPA, Hadiza Bala Usman, da ake zargi da laifi, da kafa kwamitin bincike da Minista ya yi, ya na nufin gwamnatin da APC ta ke jagorata, tana rawa dumu-dumu a cikin rashin gaskiya.

“Dauko kwamiti ya binciki zargin rashin gaskiya zai zama dabarar katange jami’an gwamnatin APC da aka samu da laifin facaka da kudi a NPA da wasu ma’aikatu.”

‘Yan jam’iyyar hamayya a majalisar wakilan suna ganin kudin da aka wawura a NPA sun haura N165b.

“Muna kira ga EFCC ta yi maza ta bi ta kan Darekta Janar da ake zargi da laifi, Hadiza Bala Usman, ta soma bincikenta, da nufin daure ta idan har an same ta da laifi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here