EFCC ta Gurfanar da Tsohon Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar tarayya ta Gusau.
 EFCC ta gurfanar da Farfesa Magaji Garba ne a gaban Mai shari’a Maryam Hassan kan laifin damfara kudi har N260m daga wurin dan kwangila.
 Tsohon malamin makarantar ya dinga tatsar kudi daga hannun dan kwangila da zummar cewa za a bashi kwangilar N3b ta katangar makarantar.
FCT, Abuja – Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranar 12 ga watan Oktoban 2021 ta gurfanar da tsohon shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba.
EFCC ta gurfanar da tsohon malamin makarantar ne a gaban Mai shari’a Maryan Hassan Aliyu ta babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, ana zarginsa ne da laifuka biyar da suka hada da samun kudi ta hanyar karya, damfara tare da takardun jabu.
 An zargi cewa ya tatsi kudi masu yawa daga dan kwangila inda ya fake da cewa zai ba shi kwangilar yin katangar da za ta zagaye dukkan jami’ar kan kudi naira biliyan uku.
Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafin ta na Facebook, hakan ya ci karo da sashi na 1, sakin layi na daya kuma abun hukuntawa karkashin sashi na 1, sakin layi na uku na laifukan damfara da laifuka makamantan hakan na 2006.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here