EFFC ta Kama Tsohon Gwamnan Jahar Abia, Theodore Orji

 

EFCC ta kama tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

Tsohon gwamnan ya jima cikin waɗanda EFCC ke gudanar da bincike a kansu tare da ƴaƴansa.

Hukumar ta na zarginsa da sama da faɗi da wasu kuɗaɗen gwamnati yayin da yake kan mulkin Abia.

Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan Abia, Theodore Orji, kamar yadda premium times ta rawaito.

Tsohon gwamnan, wanda ya jima a jerin sunayen waɗanda EFCC ke bincike a kansu, ya shiga hannu ne a filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja da misalin karfe 10:00 na safe.

Bayan samun nasarar kama shi ne jami’an EFCC suka yi gaba da shi zuwa hedkwatarsu ta babban birnin tarayya Abuja.

Yanzun haka yana tsare tare da ɗansa, Chinedu, kakakin majalisar dokokin jahar Abia na yanzu, wanda yazo bin ba’asi bayan gano an kame mahaifinsa.

Mista Orji, wanda sanata ne dake kan mulki, da ƴaƴansa biyu, Chinedu da Ogbonna, sun kasance karkashin binciken EFCC na tsawon watanni bisa zargin karkatar da dukiyar al’umma da kuma sama da faɗi da su.

Wane zargi ake wa tsohon gwamnan?

Legit.ng Hausa ta gano cewa ana zargin tsohon gwamnan da karbar miliyan N500 a matsayin kudin tsaro duk wata na tsawon shekara 8 da ya yi akan mulkin jahar Abia 2007-2015.

Sauran zarge-zargen da ake masa sun haɗa da sama da faɗi da biliyan N2bn kuɗin gwamnati da kuma karkatar da kuɗin tsarin Sure-P, kamar yadda punch ta rawaito.

EFCC ta tabbatar da tsare tsohon gwamnan

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da tsare tsohon gwamnan da kuma ɗansa kakakin majalisa, amma ya ki bada cikakken bayani.

A watan Fabrairun shekarar 2020, hukumar EFCC ta fara binciken Mista Orji da ɗansa kan zargin yin sama da faɗi da biliyan N521 tsakaninsu.

Binciken ya biyo bayan korafin da kungiyar yakar cin hanci domin ceto Najeriya ta shigar ga EFCC ranar 17 ga watan Maris 2017.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here