EFCC ta Roƙi Kotu da ta ƙwace Kadarorin Malami
FCT Abuja –Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta roƙi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaƙa da Abubakar Malami.
Kotun ta bayyana cewa tana fatan bayan an kwace kadarorin daga tsohon babban lauyan ƙasa kuma Ministan Shari’a, a mika su zuwa hannun gwamnatin tarayya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin wata takarda da lauyoyin EFCC suka gabatar ƙarƙashin jagorancin Jibrin Okutepa (SAN) da Ekele Iheanacho (SAN).
EFCC na son a kwace kadarorin Abubakar Malami
Daily Nigerian ta wallafa cewa EFCC ta shaida wa Mai Shari’a Joyce Abdulmalik cewa waɗanda ake ƙara sun kasa gabatar da hujjoji masu ƙarfi da za su sa a soke umarnin wucin gadi na ƙwace kadarorin da kotu ta bayar tun da farko.
Shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/20/2026 ta haɗa da Malami, Hajia Bashir Asabe da Abiru’ Rahman Abubakar Malami, tare da wasu kamfanoni da ake zargin suna da alaƙa da kadarorin.
EFCC ta ce ta gabatar da ƙarar ne bisa sashe na 17 na dokar zamba da sauran laifuka na 2006, tana neman kotu ta tabbatar da ƙwace kadarorin da ake zargin an samo su ne daga haramtattun hanyoyi.
Lauya Okutepa ya bayyana cewa wannan shari’a ce ta ƙwace kadara ba tare da hukuncin laifi ba, yana mai cewa kotu na da ikon doka ta amince da buƙatar.
Ya ce:
Read Also:
“Ba a gabatar da wani dalili mai gamsarwa ba da zai hana a ƙwace kadarorin gaba ɗaya ga gwamnatin tarayya.”
Abin da binciken hukumar EFCC ya gano
A cikin rantsuwar da jami’in EFCC Daniel Adebayo ya yi, ya ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe da dama kan zargin cin hanci, amfani da mukami ba daidai ba da kuma zamba a kan tsohon ministan.
Ya ce binciken ya haɗa da duba bayanan bankuna da na Babban Bankin Najeriya, da kuma bincike daga hukumomi kamar Hukumar CAC, FIRS, CCB da AGIS na Abuja.
Haka kuma an binciki rajistar filaye a jihohin Kebbi, Sakkwato da Kano, tare da tantance kadarorin a zahiri da ƙimanta su.
A cewarsa, kudin shigar Malami daga 2015 zuwa 2023 — har da albashi, alawus da kudin tafiye-tafiye — ba su kai darajar kadarorin da ake bincike ba.
Ya bayyana cewa Malami ya samu jimillar N89,664,000 a matsayin albashi, tare da N12,158,400 na alawus bayan barin aiki, sannan ya bayyana karɓar N253,608,500 a matsayin kudin tafiye-tafiye.
Sai dai EFCC ta ce yawancin kadarorin sun zarce waɗannan kudi, kuma wasu gine-gine ba su da izinin hukumomi musamman a Kano da Kebbi, lamarin da ake zargin an yi ne domin ɓoye asalin kudin da aka yi amfani da su.
An kuma zargi cewa an sayi wasu kadarorin ta hannun wasu mutane ko kamfanoni da ke da alaƙa da Malami.
Kotun ta sanya ranar 21 ga Afrilu, 2026 domin sauraron ƙarar, yayin da shari’ar ta samo asali daga umarnin wucin gadi da Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayar a ranar 8 ga Janairu, 2026, inda aka ƙwace kadarorin na ɗan lokaci da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 213.2.






