Hukumar EFCC ta Kama Tsohon Gwamnan Jahar Kwara, Abdulfatah Ahmed
Hukumar EFCC ta yi babban kamu yayin da ta kame tsohon gwamnan jahar Kwara Abdulfatah Ahmed.
Rahoto ya bayyana cewa, ana zargin gwamnan da karkatar da wasu makudan kudade mallakar jahar.
An tsare tsohon gwamnan na tsawon awanni bakwai yayin da yake ba da bayanai kan kudaden.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jahar Kwara, Abdulfatah Ahmed.
Wasu majiyoyi a hukumar sun fada wa gidan Talabijin na Channels cewa wasu gungun ma’aikata ne suka gurfanar da tsohon gwamnan a hedkwatar EFCC da ke yankin Jabi a Abuja, babban birnin kasar.
Read Also:
An ce ya isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar Litinin, a kan amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.
Bayan isowarsa ofishin hukumar ta EFCC, Mista Ahmed ya kasance a dakin bincike na kimanin awanni bakwai, yana bada bayanai.
Duk da cewa ba a samu cikakkun bayanai ba, majiyoyi sun bayyana cewa kamun nasa na da nasaba da yadda aka karkatar da wasu kudade har kimanin Naira biliyan 9 daga asusun gwamnatin jahar Kwara.
An yi zargin cewa an karkatar da kudin a lokacin Mista Ahmed da yake gwamnan jahar, da kuma lokacin da ya yi Kwamishinan Kudi a gwamnatin tsohon gwamna Bukola Saraki.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya amsa gayyatar hukumar.
Amma, ya ki karin bayani.