Gwamna Samuel Ortom ya Bayyana Gwamnan Jahar Kaduna a Matsayin Makiyin Kasar nan na Hakika

Gwamna Samuel Ortom ya bayyana takwaransa na jahar Kaduna a matsayin makiyin Najeriya.

Gwamnan na Benuwai ya kuma bayyana cewa Malam Nasir El-Rufai na daya daga cikin wadanda ke yaudarar Shugaba Buhari.

Gwamnan ya kuma bayyana abokin aikin nasa a matsayin gwarzon kabilanci kuma mai kishin addini.

Gwamna Samuel Ortom na jahar Benue ya bayyana takwaransa na Kaduna a matsayin daya daga cikin makiyan Najeriya.

Gwamna Ortom ya yi wannan ikirarin ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Terver Akase ya aika wa Legit.ng a ranar Asabar, 8 ga watan Mayu.

Gwamnan na Benuwai yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka alakanta da El-Rufai wanda ya zargi Ortom da amfani da rashin tsaro a jaharsa wajen kai hari ga gwamnatin tarayya.

Gwamnan na Kaduna ya ci gaba da cewa, Ortom yana amfani da dabaru ne domin rufe abin da ya kira gazawar gwamnan jahar Benuwai.

Sanarwar ta bayyana cewa harin da El-Rufai ya kaiwa Gwamna Ortom don kawai yayi farin jini ne a gaban fadar shugaban kasa.

Gwamna Ortom ya kara zargin El-Rufai da inganta rashin tsaro a kasar ta hanyar kalaman sa.

Wani bangare na jawabin ya ce: “Nasir el-Rufai mashahuri ne, gwarzon kabilanci, kuma mai tsananin son addini wanda yake kin duk wanda ba addinin shi daya da shi ba.

Yana cikin yan tsirarun mutanen da suka batar da Shugaba Muhammadu Buhari.

“El-Rufai na daya daga cikin makiyan kasar nan na hakika wadanda ba sa boye bambancin ra’ayinsu ta hanyar fifita son zuciya da kabilanci sama da kyawawan dabi’u da suka hada Najeriya a tsawon shekarun da suka gabata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here