Faɗa ya kaure Tsakanin Sojojin Sudan da RSF a kan Iyakar Habasha
Rahotanni na bayyana cewa ana can ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin sojojin Sudan da ƴantawayen RSF a jihar Blue Nile da ke kusa da kan iyakar Habasha.
Read Also:
Rahotanni sun bayyana cewa RSF da wasu ƙungiyoyin mayaka da ke goyon bayanta na ci gaba da kutsawa, kuma tun ranar Lahadi suka fara kai hare-hare da dama a kusa da garin Kurmuk.
Wani jami’in gwamnatin Sudan da ba a bayyana sunan sa ba ya zargi Habasha da taimakawa ƙungiyar RSF a yankin.
Addis Ababa ta buƙaci ‘yan ƙasarta da ke wannan yanki na kan iyaka da su fice.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin ta’azzarar rikicin na jefa rayukan fararen hula cikin hadari, inda aka kashe sama da mutane dari biyar a cikin watanni uku na farkon wannan shekara.






