Faɗin Gaskiya a Wannan Gwamnatin ya Zama Matsalar Tsaro – Bishop Bello

 

Malamin addinin kirista, Bishop Ransom Ballo, yace faɗin gaskiya a wannan gwamnatin ya zama matsalar tsaro.

Bala yace da zaran ka faɗi gaskiya kan wannan gwamnatin, to daga nan za’a fara bibiyarka, rayuwarka ta shiga matsala.

A cewarsa akwai bara gurbi a zagaye da shugaban ƙasa, waɗanda ke kokarin boye masa halin da kasa ke ciki.

Abuja – Shugaban kiristoci yan Calvary Life na ƙasa da kasa, Bishop Ransom Bello, ranar Talata, ya bayyana cewa yanzun faɗawa shugabanni gaskiya ya zama wani sabon matsalar tsaro, kamar yadda Punch ta rawaito.

Yace a halin da ƙasa ke cike yanzun idan aka cire ayyukan yan bindiga, satar mutane, da kuma fashi da makami, sabuwar matsalar tsaron da ta ɓullo itace faɗawa masu rike da madafun iko gaskiya.

Jagoran yace:

“Mun samu sabon kalubalen tsaro a Najeriya, idan ka faɗa musu gaskiya, zasu fara yi maka bita da kulli, kuma hakan bai dace ba.”

“Duk wata gwamnati da take son yin abinda ya dace, to wajibi ta saurari mutane kuma ta ɗauki gaskiyar da ake faɗa mata.”

“Dan me zan zama cikin tsoro don kawai na faɗawa gwamnati gaskiya kuma sun san cewa gaskiya na faɗa musu? Saboda me rayuwata zata shiga hatsari dan nace gwamnati ta gyara?”

“Kamata ya yi gwamnati ta duba da idon basira kuma ta saurari shawarwari da kuma korafin jama’a.”

Shin gwamnati na kama masu faɗin gaskiya?

Bishop Bello ya roki gwamnatin tarayya ta daina kame da kuma cin mutuncin yan Najeriya, waɗanda suka rike gaskiya komai rintsi.

“Muna da damar faɗawa masu rike da mulki da hukumomi gaskiya, matukar sun yi abinda ya dace dole mu yaba.”

“Idan kuma sun kauce wa hanya wajibi mu faɗa musu gaskiya. Amma wannan gwamnatin ta yanzun bata yin abinda ya dace, wannan shine gaskiya.”

“Zamu cigaba da faɗin gaskiya saboda akwai bara gurbi a zagaye da shugaban ƙasa, waɗanda suke kokarin ɓoye masa, ya yi tunanin yana kyautatawa yan ƙasa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here