Faransa za ta ƙwace Kadarorin Jagoran ƙungiyar Hamas

 

Faransa ta sanar da ƙwace kadarorin jagoran ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar a wani ɓangare na sabbin takunkumai da ta ƙaƙaba masa.

A cewar wata doka da aka wallafa a wata mujallar ƙasar, za a ƙwace kuɗaɗe da dukiyoyin Sinwar tsawon wata shida daga 5 ga watan Disamba,

Ba a san yawan kadarorin Sinwar a Faransa ba.

A watan da ya gabata, Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Lord Cameron ya ɗauki matakin ladabtarwa kan manyan jagororin Hamas da masu ɗaukar nauyinta

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com