Matsalar Farashin Man Fetur ta Kusan Zuwa Karshe -Gwamnatin Tarayya ga NLC

Gwamnatin tarayya ta bukaci mako daya kacal wajen kungiyar kwadago NLC domin duba yiwuwar janye karin farashin da akayiwa man fetur a watan Nuwamba.

Shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana wannan bukatar ne a ganawarsu na ranan Alhamis a fadar shugaban kasa, rahoton The Nation.

Kyari ya bayyanawa NLC cewa kamfanin NNPC kadai ba zai iya janye farashin man ba ba tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki ba.

Kungiyar NLC ta amince da hakan kuma an dage zaman zuwa ranar 7 ga Disamba, 2020.

Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnati ta janye wannan sabob kari na farashin mai da tayi saboda hakan ya sabawa yarjejejiyar da akayi a Satumba.

A karshen zaman da aka kwashe sa’o’i 3 anayi, Ministan kwadago, Chris Ngige, ya bayyanawa manema labarai cewa kwamitin za ta bayyanawa Buhari matsayar NLC tunda shine Ministan Man Fetur.

“Nan da ranar Litinin, 7 Disamba, zamu dawo, saboda sakon da yan kwadago suka zo dashi daya ne.

Suna son a janye sabon karin zuwa inda yake. Saboda haka zamu kai wannan sako wajen shugabanninmu,” Ngige yace.

Mataimakin shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero ya ce yana kyautata zaton cewa udan aka dawo ranar 7 ga Disamba, za’a janye karin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here