Farfesa Muhmood Shi ya Cancanci Cigaba da Rike Kujerar INEC – Majalisar Dattawa

 

Bayan makonni da zabensa, majalisa ta amince Farfesa Mahmoud Yakubu ya cigaba da gashi.

Farfesa Yakubu ya gaji Farfesa Attahiru Jega wanda yayi wa’adi daya kacal.

An tabbatar da shi duk da barazanar Sanatocin jam’iyyar PDP.

Majalisar dattawa a ranar Talata ta tabbatar da nadin Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC na karin shekaru biyar.

Tabbatar da shi ya biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar dattawa kan INEC karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya, ta gabatar a zauren majalisa kuma aka bukaci a amince da shi.

Sanatocin sun siffanta Farfesa Yakubu a matsayin wanda ya cancani cigaba da zama shugaban hukumar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here