Amfani da Fasahar 5G za ta Taimaka Wajen Shawo Matsalar Tsaro – Pantami
Ministan sadarwa a Najeriya ya ce gwamnatin na kokarin lalubo hanyoyin amfani da fasahar zamani wurin shawo kan matsalar tsaro, da ya hada da amfani da mutum mutumin kwamfuta.
Read Also:
Isa Ali Pantami ya shaida hakan ne yayin jawabi a wani taro kan tsaro da hukumar tsaron fararen hula ta Nigeria, wato Security and Civil Defence Corps ta shirya ranar Talata.
Ministan ya kuma shawarci hukumomin tsaron Najeriya da su rungumi damar da ta samu ta amfani da manhajar 5G wurin shawo kan matsalar tsaro.
An shirya taron ne da nufin samar da hadin kan hukumomin tsaron Najeriya wurin samar da tsaro.