Kogi Zuwa Kano: Fasinjoji 4 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyyar Hatsarin Mota
Wata motar Bas da direbanta ya gaza sarrafata ta faɗa wani kogi, inda fasinjoji huɗu suka rasa rayuwarsu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani yanki na jahar Kogi, kuma motar tana kan hanyarta na zuwa Kano.
Kwamandan jami’an tsaron NSCDC na jahar, Suleiman Mafara, ya gargaɗi direbobin kan tukin gagganci.
Kogi – Wata motar Bas mai ɗaukar mutum 18 ta faɗa kogi a Koton Karfe, jahar Kogi, inda mutum huɗu suka rasa rayuwarsu, kamar yadda Dailytrust ta rawaito.
Rahoto ya nuna cewa motar ta yi hatsarin ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare, ranar Talata da ta wuce.
Kwamandan hukumar kare haɗurra ta ƙasa (FRSC), Solomon Agure, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace motar Bas ɗin mai lamabar rijista a jahar Filato, JJN 73 XA, ta taso ne daga Ijora ƙarƙashin gada a jahar Lagos kuma tana kan hanyar zuwa Kano.
Read Also:
Agure yace mutum hudu daga cikin fasinjojin sun mutu, yayin da wasu guda bakwai suka ji munanan raunuka.
Rahotanni dun bayyana cewa direban motar ya kasa sarrafa motar ne yayin da lamarin ya faru saboda bacci ya kwashe shi.
Jami’an tsaro sun ceto wasu a raye
Kwamandan jami’an tsaro na NSCDC na jahar Kogi, Suleiman Mafara, yace bayan sun samu kiran gaggawa, jami’ansa da haɗin guiwar jami’an FRSC da yan sa kai sun kai agaji cikin sauri.
Yace:
“Jami’ai sun gano gawarwakin mutum huɗu yayin da suka ceto wasu mutum 13 a raye, sai kuma mutun ɗaya da ba’a gano ba.”
“A halin yanzun jami’an mu sun bazama neman ragowar mutun ɗaya da ba’a gano ba, kuma an kai gawarwakin da aka gano ɗakin ajiye gawa.”
Kwamanda ya gargaɗi direbobi su shiga taitayinsu
Kwamandan NSCDC ya gargaɗi direbobi da sauran matafiya da su kula da ƙa’idojin tuƙi domin gujewa faɗawa irin waɗannan hatsarin.