Gwamna Fubara na Shirin sauya sheka, Ciyamomi Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

 

Rivers – Wasu daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi na riƙon ƙwarya waɗanda Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa a jihar Ribas sun fice daga PDP.

Rahotanni sun nuna kantomomin sun sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APP a lokacin da ake shirye-shiryen zaben kananan hukumomi ranar 5 ga watan Oktoba, 2024.

Punch ta tattaro cewa an fara yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Fubara na shirin jefar da PDP, ya koma jam’iyyar APP saboda rikicinsa da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Idan baku manta ba alaƙar Fubara da magabacinsa kuma tsohon ubangidansa Wike ta yi tsami wanda ya haifar da rikicin siyasa a jihar Ribas.

Gwamna Fubara ya musanta shirin barin PDP

Duba da yadda alamu suka nuna Wike ya karɓe ragamar PDP reshen jihar Ribas, ana fara raɗe-raɗin Gwamna Fubara na shirin sauya sheka zuwa APP.

Sai dai a lokacin da ya karɓi bakuncin ƴan majalisar amintattun PDP a Fatakwal, Gwamna Fubara ya musanta duk wata jita-jitar sauya sheƙa.

Amma a halin yanzu, wasu kantomimi na tsagin gwamnan tare da magoya bayansu sun fara fita daga PDP suna haɗewa da jam’iyyar APP, rahoton The Cable.

Ƴan tsagin Fubara sun tsaya takara a APP

Kusan dukkan ƴan takarar ciyamomi da kansiloli na tsagin Gwamna Fubara sun fara shirye-shirye ne a ƙarƙashin inuwar APP duk da cewa an fara yaƙin neman zaɓe.

Tuni dai fastocin kantoman ƙaramar hukumar birnin Fatakwal, Ezebunwo Ichemati da tambarin kamfen APP suka fara yawo a kwaryar birnin.

Da yake jawabi kwanan nan, Ichemati ya yi alkawarin samar da sahihin jagoranci ga al’umma idan aka zabe shi a matsayin shugaban ƙaramar hukumar birni.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here