Wajibi ne Fulani su Bar Yankin Yarabawa Don a Samu Zaman Lafiya da Tsaro – Sunday Igboho

 

Wani matashi mai rajin kare hakkin yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya isa jahar Ogun.

Ya isa jahar ne da zafinsa don ya fatattaki kaf makiyayan da suke jahar kamar yadda yayi a jahar Oyo inda aka yi kaca-kaca da gidan Sarkin Fulani.

Ya ce wajibi ne su yaki Fulani don kawo karshen ta’addanci da cutarwar da suke yi wa ‘yan uwansa yarabawa, kuma yana da magoya baya.

Wani mai yakin kwatar ‘yancin Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa jahar Ogun yana cewa ya kai ziyarar ne don ya fatattaki makiyaya.

Dama Igboho ya bayyana a labarai yana bai wa makiyayan da suke wuraren Ibarapa dake jahar Oyo wa’adin kwanakin da za su kwashe ya nasu ya nasu su bar garin.
Bayan nan ne aka kai wa gidan sarkin fulanin yankin farmaki.

An samu labarin yadda aka lalata gidan har ana kona motocin da suke harabar gidan. Igboho ya bayyana wa manema labarai dalilin zuwansa garin.

Premium Times ta samu bidiyon tattaunawar da aka yi dashi inda yake cewa ya je ne don nema wa ‘yan uwansa hakkinsu sakamakon yadda Fulani suke ta kashe su. A cewarsa, wajibi ne Fulani su bar yankin yarabawa don a samu zaman lafiya da tsaro.

Ya ce za su wuce Yewa ne don yakar Fulanin da suke addabar yarabawan jahar Ogun.

Ya kuma yaba wa yarabawan da suka mara masa baya da kuma gwamnan jahar Ogun bisa kaunar da yake nuna wa mutanensa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here