Gwamnatin Najeriya na Shawara Kan Baiwa Fursunoni Damar Kada Kuri’a a Zaben 2023
Gwamnatin Najeriya na shawaran baiwa fursunoni dake gidajen yari a fadin tarayya daman musharaka a zaben kasa na 2023.
Sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore, ya bayyana hakan ne yayinda yake karban bakuncin kungiyar rajin kare hakin fursunoni Carmelite Prisoners’ Interest Organisation, CAPIO, ranar Talata a Abuja.
CAPIO ta kaddamar da tsarin taimakawa Fursunoni wajen tilastawa gwamnati baiwa Fursunoni hakkinsu na zabe a Najeriya.
Read Also:
Mambobin CAPIO sun garzaya ofishin Sakataren ne domin neman taimako wajen aiwatar da wannan abu, rahoton DN.
Sakataren, Shuaibu Belgire, ya bayyana cewa matsalar da suke fama shine yan bindiga na kai hare-hare gidajen gyara hali tare da sakin fursunoni.
A cewarsa, wannan ne abu daya da ka iya zama matsala ga iya amincewa fursunoni kada kuri’a.
Yace:
“Yan ta’adda na kaiwa gidajen yarinmu hari. Abinda ya zama ruwan dare kuma hakan zai iya hana baiwa mutane daman shiga (gudanar da zabe).”
“Idan babu wannan matsalan, zamu yi aiki tare da ku domin baiwa fursunoni hakkinsu na zabe.”
Shugaban kungiyar CAPIO, Rev. Fr Jude Isiguzo, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Jamus ke daukan nauyin wannan gwagwarmaya tasu.